Gidan daya 1
Wannan gidan shine gidan rayuwa, gidan wanda ke tambaya ma'ana kai karan kanka, shine gidan fara komai, a kowanne lamari, nanne gidan mahaifin mahaifiya da mahaihin uba, nanne gidan kome na matarka kai mai tambaya, saboda gidan 7 shine gidan matarka to daga gidan 7 zuwa gidan 1, taku 11 ne kaga nanne gidan komen matarka
Gidan Biyu 2
Nan ne gidan kudi, gidan dukiyar mutum sannan gidan saye da sayarwa, wannan gidan shike nuna arzikin mutum da kuma dukiyanshi
Gidan Uku 3
Shine gidan yan uwa, gidan kananan harkoki, gidan tafiya ne amma mara nisa, dalili dayasa aka kirashi da gidan harkoki da tafiye tafiye marasa nisa shine; saboda idan mutum ya samu dukiya yayi karfi to dole ne zai shagaltu da harkoki kuma ai ba'ayin harkoki dole sai anje nan da chan, sannan gidane na abokai wayanda aka yarda dasu, kuma gidane na hadaya
Gidan Hudu 4
Shine gidan iqaba qarami, ma'ana karshen lamari kenan, kuma shine gidan iyaye, gidan filaye da gonaki shuka kenan, gidan binne duk abunda ke karkashin kasa kenan, kuma nan ne gidan garin da mutum ya taso sannan garin su mutum, sannan shine gidan da ake gane wurinda barawo yayi sata sannan shine gidan dake nuna abubuwan da ke hana ko zai hana yuwuwar aure, saboda daga gidan 7 zuwa gidan 4 taku 14 ne. nan ne gidan dukiyar yan uwa, shine kuma gidan sababin rashin lafiya
Gidan Biyar 5
Wannan gidan ya'ya ne, gidan sakonni, gidan farinciki amma tsaka tsakiyar farin ciki, gidan kyan surane na mutum gidan abunci da abun sha, gidan labari ne, kuma gidan harkoki ne tsaka tsakiya, gidan tufafi ne shine gidan dukiyar mahaifi, gidan harkokin yan uwa gidan makiyan sarki, gidan abunda ke saka dukiyar matarka ke lalacewa gidane dake nuna yadda mutum ke san mata kuma gidane na shaye shaye
Gidan Shida 6
Gidan bawa, gidan rashin lafiya, nan ne gidan masu yi maka aiki ne dan a biyashi ko a biyasu, gidan sace sace ne, nan ne gidan dabbobi
Gidan Bakwai 7
Nan ne gidan aure gidan abokin takara, anan ne ake gane barawo da suffarsa gidan makiya ne wanda aka sani bawai wanda Ba'a sani ba
Gidan Takwas 8
Wannan gidan mutuwa ne gidan tsoro, kogo ne, kuma kabari ne, gidan tururuwa dake kasa kuma gidan fari ne dake bata gona, gidan guba ne tabbas, shine gidan dukiyar matarka gidan dukiyar barawo da abunda ya sata gidan mutuwar zuciya ne, gidan wasi wasi ne da shakka, gidan fitar hankali, gidan farin cikin iyaye ne, gidan sharri ne.
Gidan Tara 9
Gidan tafiye tafiye ne mai nisa kamar hajji ko daga kano zuwa lagos, kuma gidan falsafa ne da tafakkuri akan halittan duniya sannan da abunda ya shafi addinin musulunci ko kiristanci kai ko wanne irin addini, gidan mafarki ne, gidan neman ilimi ne, gidan kur'ani ne, Allahu Akbar.
Gidan Goma 10
Gidan daukaka ne, gidan mulki, gidan gobna ko sarki ko waliyi, gidan haduwa da manyan mutane, da manyan dukiya, arziki da duk wani abun da zai daga izzar shi
Gidan Sha Daya 11
Gidan Kome ne misali idan kayi tafiya nanne gidan komen ka ko in ce dawowa, gidan tsammani ne, gidan burace burace gidan abokai aminai masoya yan uwa, kuma gidan addu a ne da sa'ada
Gidan Sha Biyu 12
gidan makiya ne, gidan katsewar hanya, gidan yaqe yaqe ne, gidan husuma ne da hassada, kuma gidan makiya addini ne, gidan kurkuku ne, gidan barin gidane saboda hassada, gidan manyan dabbobi ne harda masu cutarwa, gidan kabarin yahudu ne da nasara, bola ne da duk wani abu da warinshi babu dadi, gidan tafiya ne amma a kogi, gidan tafiye tafiyen mahaifi, kurkukun makiyan sarki ne a tafiyar falaki, gidan tsoro ne na yaya maana abunda yayanka ke tsoro,
Gidan Sha Uku 13
gidan mai tambaya ne da abunda ke ranshi gidan sirrin mutum, yana karfafa gidan 1 ne,
Gidan Sha hudu 14
gidan wanda ake tambaya akan shi, kuma nan ne gidan munafukai, da abunuwan dake maida mutum baya
Gidan Sha Biyar 15
Gidan alkali, ma'ana bawai alkalin kotu ba, wannan gidan shike yin hukunci akan kasa gaba daya, shike duba hujja da yanayin mai tambaya, sannan ya duba hujja da yanayin wanda ake tambaya akanshi, sai ya yanke hukunci akan lamari, misali anyi kasa akan aure alkali wato gidan shabiyar, zai duba tauraron sha uku gidan mai tambaya yaga yanayin shi, sannan zai duba tauraron 14 gidan wacce ake tambaya akanta yaga yanayin ta, to shi zai hada yanayin su yaga sun dace ko basu dace ba, sannan sai ya yanke hukunci, zamuyi cikakken bayani akanshi nan gaba insha Allahu
Gidan Sha Shida 16
gidan karshen al'amari, wannan shike nuna karshen abunda zai kasance