IBDALI SIHIR

Duk wanda yake tunanin akwai jifa ko sharrin mayu ko kambun baka a jikinsa, to ya jarraba wannan sirrin
Bashida wahala amma kuma sai zafi, yadda ake aikin shine
Ana rubuta wayan nan ayoyin kafa 1000 kullum na tsawon kwana bakwai
Mallam insha Allahu duk jifan dake jikinka sai ya karye bi'izinillahi, ga ayoyin
وقد منا الى ماعملوا من عمل فجعلنه هباء منثورا
قال موسى ما جئتم به السحر ان الله سيبطله ان الله لا يصلح عمل المفسدين
و قل جاء الحق وزهق الباطل ان الباطل كان زهوق
Bayan an gama wannan sai kuma a rubuta ayatul kursiyu kafa 7
Rubutun wankewa akeyi asha ana saka garin habba aciki

IBDALI MAI GIRMA

Wannan sirrin yanada girma kuma yanada kyau kwarai da gaske ga masu bukatar ibdali
Indai kasan akwai jifa a jikinka to ka jarraba wannan sirrin insha Allahu za'a dace
Yadda ake aikin
Ana rubuta yasin kafa 7 amma duk aya za'a rubuta wannan ayar
وقدمنا الى ماعملوا من عمل فجعلنه هباء منثورا
In aka gama Rubutun sai a wanke a kwarya da ruwa dayawa, bayan an wanke a kwarya sai a saka

  1. Garin Habba
  2. Garin kainuwa
  3. Garin Ganyen bado
  4. Garin Kaikayi koma kan mashekiya

Bayan an saka sai a jirashi ya jika sosai to kullum za'a ke sha har tsawon kwana 14
wallahu A'alamu

IBDALI MAI GIRMA
Wannan sirrin shima na warware sihiri ne kafatan kuma yanada karfi sosai Yadda akeyinshi Ana rubuta wannan hatimin a tsakiyan rijyar sai a rubuta sunan wanda ake so a warwarewa asirin jikinshi da larabci bayan haka sai a nade layar a daura akan charbi ko kuma ka saka a gaban ka kana kallon hatimin zaka kunna wayan nan turarukan Sandal yellow, da kuma lubban zakar a kunna yana hayaki sai a yi wurudin Ya hafizu 1695 Sai wannan ayar
وقدمنا الى ما عملوا من عمل فجعلنه هباء منثورا

Kafa 1695 aikin kwana 7 insha Allahu za'a dace